Ad this

1/28/2019

[Duniyar Bishiyoyi] Ilimin kimiyya Acikin Harshen Hausa. Biyo mu don samun Ilimin kimiyya a harshen Hausa. Yau mun kawo muku bayani akan FLOWER wato sashin aihuwa na bishiyoyi. Shiga...........

[Duniyar Bishiyoyi] Ilimin kimiyya Acikin Harshen Hausa. Biyo mu don samun Ilimin kimiyya a harshen Hausa.


Yau mun kawo muku bayani akan FLOWER wato sashin aihuwa na bishiyoyi. Shiga...........


         FURE (FLOWER)
Menene Fure (flower): Fure (flower) wani sashi ne na haihuwar shuka wato (plant) a turance, Wanda suke karkashin ajin (magnoliophyta) a kashin (angiospermae) wato tsirrai masu fitar da fure (flower). Ana amfani da wannan Kalmar ta fure (flower) musamman idan wani bangare ko kuma duka bangarorin haihuwa masu launi da sifa suka bayyana.
   A bangaren launi, girma, sifa da yanayin tsarin fannonin jikinsu, fure (flower) sunada hade-haden launi marar iyaka. Sun fara daga kananu zuwa manya. A wasu shukokin kamar su poppy, magnolia, tulip da Petunia, Kowa ne fure (flower) acikin su babba ne kuma suna Samar da guda daya ne, amma a wasu shukokin kamar su aster, snapdragon, calla lily, and lilac. Fure (flower) daya yana kasancewa da banbance- banbance a tsakaninsu Kowa ne fure(flower) suna da amfani iri daya ne, shine haihuwar irin su a sakamakon Samar da iri wato (seed) a turance.
       
        SASSAN FURE (FLOWER)

* PEDUNCLE: Shine ginshikin fure (flower) ko kuma karan dayake kasan fure (flower)

*RECEPTACLE: Shima wani bangaren ginshikin fure(flower) ne Wanda suke manne dashi.

* SEPAL: Shine fure (flower) na farko Wanda ake ganinsa ta waje, yananan Kore ne kamar ganye a halittarsa kuma yana kunshe da fure (flower) Sabon toho acikinsa.

* PETAL: Shine sashi na fure (flower) da ke dauke da launi mai jan hankali.

* STAMEN: A nan ne ake Samar da pollein wato kwayoyin haihuwar namijin fure (flower) yawanci yana cikin wani halitta dogo, siriri kamar kara Wanda ake kira da filament a turance.

* ANTHER: wàni sashi ne ajikin stamen inda ake Samar da kwayar pollein.

* PISTIL: A nan ne ake Samar da ovule wato kwayar haihuwar jinsin tamacen fure(flower) . Acikinsa akwai fannoni kamar su ovary, style, stigma. Idan ovary ya girma shi yake zama Dan itace (fruit), idan kuma ovule ya girma shi yake zama iri wato (seed).

* STIGMA: wani sashi ne na pistil wato mace fure(flower) in da pollein yake girma.

* OVARY: Shine sashi mafi girma a pistil in da ake Samar da ovule.
   
      Duk furen (flower) da yake dauke da fannoni kamar sepals, petals, stamens, da pistils shi ake kira cikakken fure (flower), idan kuma ya rasa daya daga cikin wadannan ko fiye da haka ana kiran shi da incomplete flower ko furen da ba cikakke ba.
   
    Stamens da pistils ba'a samun su a ko wane fure (flower), idan kuma aka samesu ajikin fure (flower) daya, wannan fure (flower) ana ce mishi (perfect flower) cikakken fure ko kuma (bisexual flower) shine furen mai dauke da sashin haihuwa guda biyu.
   
    Akwai furen da bayida stamen ana ce mishi pistillate, ko kuma Tamacen fure. Haka kuma furen da bayi da pistils ana ce mishi staminate ko kuma namijin fure.
     Akwai furen (flower) da yake dauke da bangarorin jinsin maza da mata a jikin bishiya daya ana kiransa da monoecious flower.
    Haka kuma Wanda jinsin namiji da na mace yana jikin bishiyoyi daban-daban ana ce mishi dioecious flower.

Anan zamu gintse da fatan an karu an samu haske.

Muna sauraron ra'ayin ku game da shirye-shiryen mu.


Abusulaym111
28-01-2019.

No comments:

Post a Comment