Ad this

7/29/2019

[DUNIYAR BISHIYOYI 001] SHIGA NAN DOMIN GANIN YADDA BISHIYOYI KE HAIFUWA CIKIN YAREN KA NA HAUSADuniyar Bishiyoyi 001
Yadda bishiyoyi masu Flower suke haihuwa wadda a turance ake kira da REPRODUCTION SYSTEM IN FLOWERING PLANTS.

ZAMU CI GABA DA KAWO MUKU WANNAN DARASI DOMIN SAMADDA KYAKKYAWAR ALAƘA DA GYRAN MUHALLIN MU.

BISHIYOYI SUNA DA MATUKAR MUHIMMANCI A MUHALLIN MU TA YADDA SUKE SAMAR MANA DA ISKA NA SHAƘA, RAGE ZAFI, SAMAR DA INUWA, RAGE ZAI-ZAIYEN ƘASA, SAMAR DA ABINCI DA SAURANSU.

ZAMU FARA BAYANI AKAN MENENE FLOWER.
FLOWER : ITACE GAƁA NA HAIFUWA AJIKIN BISHIYOYI. TANA DAUKE DA NAMIJI DA NAMIJI AJIKIN TA KUMA ITACE BABBAR HAƊEDƊIYAR GAƁA NA HAIFUWA A DUNIYAR BISHIYOYI. AKAN SAMU FLOWER KALA-KALA, GIRMAG-GIRMA KAMAR JA' , RUWAN DORAWA (YELLOW) DSS.

FLOWER: hadaka ce ta ganyayyaki wadda aka yi musayar su zuwa gaɓar haifuwa dore a saman sandar Flower (pedicel).

FLOWER tana da ɓangarori ko katanga (whorls) guda Hudu (4). Gasu kamar haka:
1. Katanga ta farko ta waje (Sepals)
2. Katanga ta biyu (Petals)
3.  Ɓangaren haifuwa na namiji (Stamens)
4. Ɓangaren haifuwa na mace (Carpels)

An kasa bangarorin guda biyu:
Akwai mai muhimmanci sosai:
1. Stamens
2. Carpels
Akwai mai muhimmanci kadan:
1. Sepals
2. Petals
Duka bangare hudun suna jere ne ɗaya bisa ɗaya akan thalamus.
 Anan zamu dagata sai kuma rubutu nagaba a Duniyar Bishiyoyi 002

#duniyar
#Bishiyoyi
#gsu
#Biology
#education
#Gombe
#arewa
#nigeria


Ibrahim Ali
Tolba
30/07/2019

No comments:

Post a Comment